Kalubali Ta Yaya Rayuwar Mata-Maza Ke Kasancewa a cikin Rayuwar Al’umma a Duniya
Akan haifi wasu da halittar jinsi biyu, na mace da na namiji
– Wasunsu sukan girma su zama ‘yan daudu
– Da yawa a al’umma suna shan tsangwama
Yaya rayuwar Mata-Maza take a tsakanin al’umma?
Malam Rikadawa a wani fim
A al’umma a kowacce nahiya, ana samun Mata-maza, watau mutane wadanda su ba mata bane, ba kuma maza ba, kuma dukka biyun ne, watau suna da halittu na maza kuma suna da na mata, sai dai ba safai sukan nuna kansu ba, musamman idan suna tsoron tsangwama daga jahilai.
Yaya rayuwar Mata-Maza take a tsakanin al’umma?
Hoto daga Getty ta hannun BBC
A kasashen Turai dai irin hakan kan kai wadannan mutane ga likita, domin a maishe su mata cikakku, ko maza cikakku, idan sun balaga, sun kuma duba ko wanne jinsi ne ya fi karfi.
A kasashen mu na Afirka kuwa, saboda rashin gane yadda lamarin yake, irin wadannan mutane kan sha wahala, in ba a gida ba, a gidan aure, in ba a nan ba, a wurin al’umma, in kuma ba a nan ba, a wurin jahilai.
Wannan ne yasa da yawansu sukan koma zama gidan karuwai, da sunan ‘yan daudu, ko masu barkwanci, saboda a irin wannan dandali, kowa baya tsangwamanr wani, kamar dai a wadannan wurare an fi iya jure wa baare.
Da zarar balaga ta iso, wadansu cikin su sukan fara ganin al’ada ta mmace, kuma muryarsu ta koma ta mata, su ringa rangwada da yin hali irin na mata, su ma iya ganin nonuwa sun fito musu, duk da cewa a al’umma ana dauka da gangan suke hakan.
An dai sami addinai da suke haramta irin wadannan mutane da rayuwa cikin al’umma, domin a lokutan da suka gindaya sharuddansu, basu fahimci irin wannan halitta ba, musamman sinadarai kamar su Oestoegen da Testostherone sinadarai da su suke fadi wa kwakwalwa ko mutum namiji ne ko mace, kuma wanne jinsi yake/take sha’awa domin saduwa.