Uncategorized

INA YAWAN SABON ALLAH, MENENE SHAWARA ? | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

INA YAWAN SABON ALLAH, MENENE SHAWARA ?

Tambaya :
Salam, malam a cikin zuciya ta ina jin tsoron Allah,kuma ina son bin umarnin Allah, saidai ina yawan sabon Allah kuma, malam ina so a taimake ni da shawara akan hakan ?

Amsa:
To dan’uwa, ina fatan za ka karanta wannan kisar da idon basira, domin za ka samu shawarar da kake bukata :
Wani saurayi ya je wajen Ibrahim dan Adhama, (daya daga cikin magabata), sai ya ce masa zuciya ta tana tunkuda ni zuwa sabo, ka yi min wa’azi, sai ya ce masa :
Idan ta kira ka zuwa sabawa Allah to ka saba masa amma da sharuda guda biyar, sai saurayin ya ce fadi mu ji :

1. Idan za ka sabawa Allah, to ka boye a wurin da ba zai ganka ba, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za’a yi na boye masa, alhalin babu abin da yake buya gare shi, sai ya ce : yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali kuma yana ganinka.

2. Idan za ka sabawa Allah to kar ka saba masa a cikin kasarsa, sai saurayin ya ce : tsarki ya tabbata ga Allah, ina zan je, alhali duka duniya ta sa ce, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali kana zaune a saman kasarsa.

3. Idan za ka sabawa Allah to ka daina cin arzikinsa, sai saurayin ya ce : tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni’imomi daga gare shi su ke, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali yana ciyar da kai kuma yana shayar da kai, yana ba ka karfi. 

4. Idan ka sabawa Allah, to idan mala’iku suka zo tafiya da kai wuta, ka ce ba za ka tafi ba aljanna za ka, sai saurayin ya ce : tsarki ya tabbata ga Allah ai sun fi karfina, kora ni za su yi.

5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar alkiyama ka ce : ba kai ka aikata su ba, sai saurayin ya ce : tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala’iku masu kiyayewa, sai ya fashe da kuka ya tafi yana maimaita wannan Kalmar ta karshe.

IN HAR KANA TUNA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN IDAN ZA KA AIKATA ZUNUBI, TO TABBAS ZA KA JI KUNYAR ALLAH
   Amsawa
Dr jamilu yusuf zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button