Uncategorized

Abu shida Da ma’aurata Za Suyi Yi Bayan Gama Jima’i (saduwa) musamman mace…..

A bisa al’ada na zamantakewan aure tsakanin ma’aurata da zaran sun gama saduwa sukan yi hira ne a tsakaninsu game da jima’in da suka yi ko kuma wani batun na daban ko kuma su kwanta bacci.

Hakan bai ‘baci ba toh sai dai akwai wasu abubuwa da ya kamata su yi bayan gama saduwa wanda hakan na iya karesu daga kamuwa da wasu cutututuka da kuma tsaftan jiki.

Ga abubuwa da za su yi bayan gama jima’i.

1. Fitsari: Kada ku manta ku yi Fitsari domin zai taimaka wurin hana kwayan cuta zama a maranku. Yin fitsari da zaran an gama saduwa na wanko wasu kwayoyin cuta da ke cikin farji.

2. Shan Ruwa: kada ku manta ku sharuwa da zaran kun kammala saduwa a wannan dare domin nan ne kwayan cuta zai samu daman bi fitsari zuwa waje.

3. Kada ku yi bacci da kaya da suka matse jikinku. Kaman gajeren wando, dan kamfe ko kuma rigar mama da dai makamantansu domin a wannan lokaci al’uranku na bukatan hutu ba takura ba. 

4. Wanka da Sabulu (Kunfa): A guji wanka da duk wani nau’in wani abu mai kumfa musamman ga mace domin bayan gama saduwa farji ya riga da ya bude ko kuma a ce ya bulluko, dan haka ya zama dole a kiyaye amfani da kumfa wurin wanka gudun kada kumfan ya shiga ciki domin ya na iya kai damuwa ga farji.

5. A yi amfani da ruwa maimakon maimakon goge jiki.

6. A samu wani abu mai madara-madara a sha ko a ci domin hakan zai kara kuzarin jiki.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button