Uncategorized

MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA

Tambaya :
Malam idan ya zama mace ba ta yin haila sai duk bayan wata uku, yaya idarta za ta kasance ?

Amsa :
To malam dole ne, sai ta yi jini uku kamar yadda Hanafiyya suka fada, ko kuma tsarki uku kamar yadda Malikiyya suka tafi akai, ko da kuwa duk shekara take yin haila sau daya,

saboda Allah madaukaki ya rataya idda ne da samuwar jini, kamar yadda yake cewa a cikin suratul Bakara aya ta : 228 “Kuma matan aka saka, to za su jira tsawon jinane uku”

DON HAKA DUK TSAWON LOKACIN DA ZA TA ZAUNA TO DOLE SAI TA JIRA SU, KAMAR YADDA AYAR TAKE NUNAWA.
Allah ne mafi sani.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button