Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Zai Maka Jaridar Charlie Hebdo Kotu
DAGA S-bin Abdallah Sokoto
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya lashi takobin daukar matakan shari’a a kan jaridar Charlie Hebdo, bayan zanen batacin da ta yi na shugaba Recep Tayyib Erdogan.
Kafafen watsa labaran cikin gida a Turkiyya sun rawaito cewa tuni masu gabatar da kara a Turkiyya sun fara kaddamar da bincike a kan jaridun da suka kira ”Shaidanun’, wato jaridun da ke wallafa zanen barkwanci da ke nuna Annabi Muhammad.
Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin Faransa da Turkiyya, bayan kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron na goyon bayan wani zanen batanci da ya nuna Annabi Muhmmad
Hakama shugaba Erdpgan ya yi kira ga kasashen musulmai a fadin duniya su kauracewa kayayyakin da Faransa ke samarwa, a wani salo na yi wa kasar taron dangi.
Ubangiji Allah ya baiwa Erdogan nasara akan wadannan makiya musulunci.

