Addini

Ba Zama ! Ya Allah Ka tsinewa shugaban kasar Faransa Emanuel Macron – Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun

DAGA Dokin Karfe TV
Babban malamin addinin musuluncin nan a Najeriya, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya la’anci shugaban kasar Faransa Emanuel Macron bisa batancin da yayi ga fiyayyen halitta annabi Muhammad (S.A.W).
Shehin malamin ya tsinewa Macron ne yau Alhamis a lokacin da yake gabatar da karatun bayan sallar Asuba don kare martabar manzon Allah (S.A.W) a masallacin dake kofar gidan sa a garin Rigachikun Kaduna, inda yace: “Allah ya tsine wa shugaban kasar Faransa Emanuel Macron Albarka”
A yayin karatun, malamin addinin ya kuma ambaci martabobin manzon Allah (S.A.W) tare da ambaton fifikon da Sahabbansa suke dashi saboda sun taimake sa wajen yada Addinin musulunci.
“A don haka muna rokon Allah ya tsine masa albarka” Inji malamMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button