Gwamnan Bauchi sanata bala ya biya rabin cikon kuɗin alhazzan jihar bauchi


Biyo bayan karin kudi da anka samu daga hukumar kula da alhazzai ta kasa NAHCON ta sakar a makon da ya gabata akan kowa ya biya 1.9miliyan bayan wanda ya biya naira miliyan 4.9.
Wanda kuma zai biya a yanzu da bai bada ko sisi ba zai bada Naira Miliyan takwas da dubu dari biyu da yan dori kamar yadda sunka fitar da sanarwa.
Shine gwamnan jihar Bauchi sanata bala Muhammad kauran bauchi ya fitar da sanarwa a shafinsa na sada zumunta cewa inda yake cewa.
“Jama’a barkan mu da Juma’a, yaya Ibada?
La’akari da halin ƙunci da tsadar rayuwa da muka tsinci kan mu a ciki, na sanar da biyan rabin ƙarin kuɗin da hukumar kula da jin daɗin alhazai ta ƙasa wato NAHCON ta buƙaci kowane maniyyaci ya biya.
Na biya wa kowane maniyyacin jihar Bauchi tallafin naira dubu ɗari tara da hamsin, wato kaso 50% na ƙarin kuɗin, sannan na umurci hukumar a matakin jiha da ta mayar wa kowane maniyyaci kwatan-kwacin tallafin da muka biya, waɗanda ba su biya ƙarin ba kuma su cire kafin cikar wa’adin da aka ɗiba.
Allah ya ƙara sauƙaƙa mana, ya sa mu yi ibada karɓaɓɓiya.”
Tabbas wannan abun ayaba ne duba da irin yadda halin rayuwa da ake ciki wanda ya sanya wani yayi iya kokarinsa domin sauke farali amma sai yaji ƙarin kuɗi kwatsam.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





