Yanzu-yanzu: Yan Shi’a sun bankawa ma’aikatar NEMA wuta
A yanzu haka, wani sashen ma’aikatar hukumar bada agaji na gaggawa ta kasa wato NEMA dake Abuja na ci bal-bal.
Hakazalika an bankawa motocin hukumar biyu wuta kuma jami’an kwana-kwana na cikin kashe wutan yanzu.
A cewar The Cable, Wani mai idon shaida ya bayyanawa manema labarai cewa yan kungiyar Shi’a mabiya Sheik Ibrahim El-Zakzaky da suke gudanar da zanga-zanga suka bankawa ma’aikatar wuta lokacin da yan sanda suka hanasu zanga-zanga.
Zanga-zangar wacce suka fara daga tashan NITEL Junction dake Wuse 2 ya samu cikas ne yayinda yan sanda suka toshe hanyar zuwa majalisar dokokin tarayya da fadar shugaba kasa
Kawai sai yan sanda suka fara harbe-harbe yayinda yan Shi’an ke kokarin shiga farfajiyar Eagle Square. Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu kawo yanzu.
Wani dan Shi’a yace: “Za mu cigaba da zanga-zanga, kuma idan basu son ganinmu a kan titi, gwamnati ta saki shugabanmu. Idan suna son kashe, su cigaba da kashemu.”
![]() ![]() |
| Gawar da anka kashe |
HAPPENING NOW: National Emergency Management Agency (NEMA) shed/outpost set ablaze by Shi’ite members in Abuja. pic.twitter.com/UJiFseMPWc— TVC News (@tvcnewsng) July 22, 2019

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






