Bilitin halal ne a Musulunci- sheikh Ibrahim Khalil


Shugaban Majalisar Malaman Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya ce Bilitin halak ne a Musulunci a wata zata zantawa da gidan rediyo freedom sunka da shehin malamin addinin musulunci inda yake cewa.
“Shi bilitin ba haramun bane sai dai idan har zai cutar da fata ko lafiyar jiki to a nan ya zamo haram ko a yaushe idan namiji ko mace zatayi bitilin to kamata yayi yaje ya tambayi likita ya nuna masa irin man da zaiyi amfani da shi ko sabulu zaiyi amfani da shi ba komai, shi abinda ake magana yinsa shi ba laifi bane.
Amma abinda yake sanya cancer ko na ɓata fata ko hallita ko mutum ya jefa kansa shine haram ko makaruhi, kuma shi abinda mutane basa ganewa ai shi annabi adam baƙi ne , hauwa’u fara, to me asara dan ka zamo kamar babanka ko ka zamo kamar uwarka , fari baifi baki ba, baki bai fi fari ba, ae in ma lafiya ce baki yafi fari lafiya.”-inji sheikh khalil
Shin maza zasu iya yin bilitin?
Namiji zai iya yin bilitin mace zata iya yin bilitin sai dai suje su nemi shawarar likita na fata ya fitar musu da wanda ya dace da wanda bai dace ba, da allura da sabulu da mai duk za’a iya amfani da su”– inji sheikh Khalil.
A arewacin Najeriya arewa maso yamma kamar yadda ƙididdiga masana na nuna babu inda yakai yawan yan mata masu bilitin irin jihar kano duba da irin yadda jihar take da yawan mutane, zaka ga budurwa wata kala amma zuwa wani lokaci ta koma fara duk shafe shafen man bilitin ne ya maida wasu farare a jihar, wasu mazan ma suke saiwa matansu kayan bilitin.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




