Tsadar Rayuwa: Tsohon Shugaban Kasa Ya Yi Magana, Ya Bayyana Abin da Ya Ke Tsoron Zai Faru


Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana kan mawuyacin halin kunci da ‘yan kasar ke ciki na tsadar rayuwa Tsohon shugaban kasar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki Janar din ya bayyana haka ne a yau Juma’a 16 ga watan Faburairu a shafinsa na X kan irin halin kunci da ake ciki
Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya yi magana kan halin da ake ciki a kasar. Ibrahim Badamasi ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki na mawuyacin hali.liberty tv na ruwaito.
Mene tsohon shugaban ke cewa ga Tinubu?
Tsohon shugaban ya ce ba ya goyon bayan juyin mulki a kasar amma kuma dole Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta taimaki ‘yan kasar. Ya ce idan har gwamnatin ba ta dauki matakin kawo dauki ga ‘yan kasar ba komai na iya faruwa. Ya kuma bukaci Shugaba Tinubu ya dauki tsauraran matakai da za su dakile matsalar kafin komai ya rikice a kasar. A cewarsa: “Ba na goyon bayan karbar mulki daga hannun farar hula, amma ina rokon Gwamnatin Tarayya ta kawo dauki ga ‘yan Najeriya.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





