Labarai

AL’AJABI: Ɗaya da ga cikin ɗaliban Bethel da a ka sace ya ce ya fi jin daɗin zama da ƴan fashin daji/yan bindiga

AL'AJABI: Ɗaya da ga cikin ɗaliban Bethel da a ka sace ya ce ya fi jin daɗin zama da ƴan fashin dajiƊalibi ɗaya tilo da ya yi saura a hannun ƴan fashin dajin da su ka yi garkuwa da ɗalibai 121 na Makarantar Bethel Baptist High School a Jihar Kaduna ya ce ya fi jin daɗin zama a hannun ƴan ta’addan.
A tuna cewa a ranar 5 ga watan Yulin 2021 ne ƴan ta’addan su ka kutsa kai cikin makarantar da ke kan titin Kaduna-Kachia, a ƙauyen Damishi, da ke Ƙaramar Hukumar Chikun su ka yi awon-gaba da ɗaliban.
Jaridar Daily Nigerian da Vanguard sunka rawaito cewa Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa, CAN, reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab ne ya baiyana hakan.
A cewar Hayab, duk da an biya kuɗin fansar sa, ɗalibin ya kafe ya ce shi ba zai dawo gida wajen iyayen sa ba.
“ɗalibi ɗaya da ya yi saura a hannun ƴan fashin daji, wanda shi ne mafi kankanta a cikin su, ya ce ba zai dawo gida ba.
“Ya ce shi zai ci gaba da zama da ƴan fashin dajin. Wannan abin al’ajabi ne ga ɗaukacin ƴan ɗariƙar Baptist da ma CAN baki ɗaya.
“An ce wai ƴan ta’addan na bashi kyautar kayaiyaki ne duk sanda su ka je su ka kai hari su ka dawo, shi ya sa ya ki yadda ya dawo gida.
“Ina ganin wayo su ka yi wa yaron su ka riƙa bashi kayan daɗi domin su yaudari zuciyarsa ya ji baya son komawa gida. An ce wai yaron ya ma gaya musu cewa shi ba ya son komawa wajen iyayen sa saboda wai dama dukan sa a ke yi gida idan yai laifi.
Hayab ya ƙara da cewa shima mutumin da ya saba kai wa ƴan ta’addan kuɗin fansa sun riƙe shi bayan da ya ke kai kuɗin fansar shi wannan yaron da ya ce ba zai dawo ba.
“Gaba ɗaya ma lamarin ya jefa mu cikin ruɗani. Shi mutumin da ya saba kai musu kuɗaɗen fansa, ko me ya faru?, ya je kai kuɗin fansar shi wannan yaron, ƴan ta’addan sun riƙe shi.
“To gaba ɗaya lamarin ya ɗauki wani sako na daban. Mu na dai roƙon Ubangiji ya kawo mana ɗauki,” in ji Hayab.
Ya kuma yi kira ga mahukunta da su dage su ƙwato yaron nan da ga hannun ƴan ta’adda da ma sauran mutanen da a ka yi garkuwa da su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button