Farashin Kayan Abinci A Wasu Kasuwannin Jihar arewacin Nijeriya yayi tashin gwauron zabi


A wannan sati kayan abinci yayi tashin gwauron zabi inda buhun Shinkafa da masara, da dawa sunkayi wani tashi abun sai addu’a inda farashin Shinkafa yake son kai naira dubu ɗari da hamshin, kamar yadda majiyarmu ta Katsina Reporters na ruwaito.
Kasuwar garin Kankara, ga yadda farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara – 62,000_ 63,000
2- Buhun Dawa – 58,000
3- Buhun Gero – 60,000 Dauro – 49,000
4- Buhun shinkafa – 120,000 ta tuwo – 130,000
5- Buhun Gyada ‘yar Nijer – 85,000 ‘yar yawuri – 120,000 ‘yar zamfara – 120,000
6- Buhun wake – 84,000_ 85,000
7- Buhun Waken suya – 54,000 _ 55,000
8- Buhun Alkama – 66,000
Kasuwar garin Ingawa,ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun Masara – 59,000 ja – 60,000
2- Buhun Dawa ‘yar kudu – 56,000 Mori – 54,000 Fara – 52,000 ta gida – 51,000
3- Buhun Gero – 54,000
4- Buhun Maiwa – 54,000
5- Buhun Shinkafa – 83,000 shenshera – 30,000
6- Buhun Gyadar kulli – 78,000 kwankwasa – 28,000
7- Buhun Alabo – 38,000
Kasuwar garin Danmusa, ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun Masara – 60,000
2- Buhun Dawa – 48,000
3- Buhun Gero – 40,000
4- Buhun Shinkafa samfarera – 32,000
5- Buhun Gyada tsaba – 80,000 _ 90,000 Mai bawo – 30,000
6- Buhun Waken suya – 55,000
7- Buhun Wake – 79,000 _ 80,000
8- Buhun Tattasai – 28,000
9- Buhun Aya manya – 47,000 kanana – 38,000
10- Buhun Dabino – 100,000
11- Buhun Albasa 70,000
Kasuwar garin Ajiwa a Karamar Hukumar Batagarawa, ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun masara – 60,500 2- Buhun Gero – 58,000
3- Buhun Dawa – 54,000
4- Buhun Gyada – 130,000
5- Buhun wake – 90,000
6- Buhun waken suya – 55,000
7- Buhun Alabo – 42,000
8- Buhun Kwaki ja – 28,000
9- Buhun Dankali – 22,500
Kasuwar garin Mararrabar Kankara a karamar hukumar Malumfashi,ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun masara – 59,000
2- Buhun Dawa – 46,000
3- Buhun Dauro – 54,000
4- Buhun Gyada – 100,000
5- Buhun Shinkafa tsaba – 100,010 shanshera – 34,000 _ 35,000
6- Buhun Wake – 82,000
7- Buhun waken suya – 56,000
8- Buhun Garin kwaki – 30,000
9- Buhun Alabo – 45,000
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





