Labarai

Wata Budurwa Ta Bude Sabon Guruf a Whatsapp, Ta Zuba Samarinta, Ta Fada Musu Aure Zata Yi

Wani matashi ɗan Najeriya ya bayyana yadda budurwarsa ta yaudare shi a wani rahoto da jaridar Legit.ng ta wallafa.Saurayin mai suna Prince Mudi yace budurwar ta buɗe sabon dandali (Group) a Whatsapp sannan ta saka shi a ciki.

Wata Budurwa Ta Bude Sabon Guruf a Whatsapp, Ta Zuba Samarinta, Ta Fada Musu Aure Zata Yi
Wata Budurwa Ta Bude Sabon Guruf a Whatsapp, Ta Zuba Samarinta, Ta Fada Musu Aure Zata Yi

Amma sabon Guruf ɗin da ta bude ya kunshi baki ɗaya samarinta saboda tana son haɗa su a wuri guda.

Sai dai manufarta a zuciya shi ne tana son rabuwa da su baki ɗaya kana ta ci gaba da rayuwarta da sabon saurayin da zata aura.

Meyasa ta rabu da samarin baki daya?

Prince Mudi ya ci gaba da cewa bayan ta gama tattara su sai ta sanar musu cewa aure zata yi. Daga nan kuma ta fice daga Guruf ɗin.

Prince Mudi yace:
“A 2017 na yi soyayya da wata yarinya tsawon shekara ɗaya. Wata rana kawai ta saka ni a Guruf ɗin Whatsapp tace ‘Ku ne mutanen da bana so kuma komai ya zo karshe saboda zan yi aure karshen mako mai zuwa.”
“Ba wata-wata ta fice daga Guruf ɗin ta barmu nan muna kokarin sanin juna.”

Mutane sun yi martani

@ohlynxx93 yace:
“Abun jin daɗin shi ne mai yuwuwa ɗiyarta ce zata sha wahata ta girbi laifin da mahaifiyarta ta tafka.”

@the_saintmusty yace:
“Haba ku bar komai kowa ya cire kuɗi ya siyo sabon kaya, ku halarci bikinta a matsayin ƙawayen amarya.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button