Labarai

Bani da alaka da wadanda suka daukaka kara a kai na – sheikh Abduljabbar

Advertisment

Malamin nan Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara, ya nesanta kan sa da mutanen da suke yunkurin daukaka kara a kan hukuncin da aka yanke masa a baya.

Abduljabbar ya bayyana hakan ne ta cikin wata takarda da ya rubuta mai kwanan wata 07 02 2024, aka aikwa manema labarai.

Dala fim na ruwaito Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara ya bayyana cewar bashi da wata alaka da mutanen da ake bayyana kansu a matsayin almajiransa.

Ya kuma bayyana cewar wannan yunkurin da masu niyyar daukaka karar suke yi ba da yawunsa suke yi ba.

Idan dai ba’a manta ba babbar kotun shari’ar muslinci ta kofar kudu ce dai ta yanke hukuncin kisa akan malamin sakamakon samunsa da laifin batanci ga Annabi S.A.W, tun a baya.

Wakilinmu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa a makon da zamu shiga ne babbar kotun jaha za ta fara sauraron bangarorin da suka shigar da karar da kuma bangaren gwamnati.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button