kotu ta tabbatar wa gwamna Dauda kujerar gwamnan Zamfara


Matawalle ya sha ƙasa a kotun Koli, kotu ta tabbatar wa gwamna Dauda kujerar gwamnan Zamfara
Kotun Koli ta tabbatar wa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal na Zamfara kujerar sa na gwamnan jihar.
A hukuncin da kotun Koli ta yanke a ranar Juma’a ta ce kotun Ɗaukaka kara sun tafka shirme a hukuncin da suka yanke da cire gwamnan da kuma sanar da sake zaɓe a wasu kananan hukumomi.


Maisharia Emmanuel Agim wanda ya karanta hukuncin a madadin alƙalan kotun ya bayyana cewa kotun ɗaukaka kara ba ta yi abinda ya dace ba ” Sabida haka kotun koli ta jaddada wa Lawal kujerar sa na gwamna Zamfara.
Wani labari : Ƴan bindiga sun kai wani ƙazamin hari wanda yayi sanadiyar rasuwar rayuka da yawa a kastina
Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe Mai gari da ɗansa da wasu mutune taƙwas a kauyen Kukar Babangida da ke Karamar Hukumar Jibia a Jihar Katsina.
Kamar yadda Katsina Reporters ta samu, a daren ranar Laraba ne ’yan bindigar suka yi wa mutanen ki-san gilla, ciki har wani mai gadi da suka yi wa yan-kan rago.
Wani dan yankin da ya nemi a boye sunansa ya ce, zugar ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 10 na dare, inda “suka ka-she mai gari Magaji Haruna da dansa Idris, tare da wasu mutane uku a gidansa.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



