Labarai

Darasin Dauka Akan R Kelly : kotu ta yankewa Mawaki R Kelly Shekaru 30 a Gidan Yari

Robert Kelly, wanda duniya tafi sani da suna R Kelly, mawaki ne daya fice a duniyar mawaka na kasar Amurka. Mawaki ne da ya samu daukaka da kuma baiwar iya waka da ake kira a turance R&B.
A ziya ne wata kotu a kasar ta Amurka ta dauke mawakin Dan Shekaru 55 da haihuwa har tsawon shekaru 30 saboda samun sa da laifuka guda 9 da ake zargensa ciki har da safaran kananan mata da kuma tilasta musu yin zina da kuma yi musu Fyade.

‘Yan matan da suka bada sheda a gaban kotu ne sunyi bayanin yadda shararren wamakin yayi ta yaudaransu da zai zama manajansu amma daga bisani sai yayi lalata dasu ya watsar da su. Akwai wata ma data bada shedar tare da tunatarwa da mawakin yadda ya sata tayi ta tsotsan gabansa da duburansa duk domin son ya sakata a cikin yaransa domin nan gaba ita ma tayi fice.

Abun tashin hankali game da irin wadannan matan da suka bautu a karkashin Kelly wasu ma har mutuwa sunyi, wasu kuwa sun shiga shaye shaye ganin yadda burin da suke dashi na zama mawaka ya kasa cimmuwa.
Akwai wadanda har sun girma sunyi aure amma sai gashi sun fito suna bada shedar irin abunda Robert yayi musu suna matasa.
Wani abun Allah wadai da wannan cin zarafin da yayiwa matan nan cikinsu kananan yara masu karancin shekaru daga 12 zuwa 15 sun fi yawa saboda shi mutum ne mai sha’awar lalata da :yan shela kamar yadda wata take fadi.Darasin Dauka Akan R Kelly : kotu ta yankewa Mawaki R Kelly Shekaru 30 a Gidan Yari

Idan muka duba irin wannan halin da R Kelly yayiwa yara mata masu sha’awar zama wani abu duniyar waka. Inda yayi amfani da matsayinsa a duniya na Selebiriti ya baida su bayi ba tare da tunanin za a wayi gari wata rana ya samu kansa a halin da yake ciki a yanzu ba. Haka nan wasu Selebiriti na wasannin Hausa da dama suke yiwa ‘yayan mutane a yanzu haka. Ganin ‘yan matan basa iya fitowa fili suyi magana, yasa suke ci gaba da wannan halin irin na Kelly koma fiye.

Nasan yaran mata kanana da manyan da wasu furodusoshi Selebiriti suka lalata musu rayuwa kuma suka kasa cika musu alkawari na sasu a finafinai. Bama manyan mata masu hankali da wayo ba, akwai Yara da dama masu karancin shekarun da yanzu haka suna karkashin bautar furodusoshi da celebrities na wasannin Hausa ko mawakan Hausa wanda idan zan kawo rahoton abunda yake faruwa ko halin da suke ciki mutane zasu fahimci shi R Kelly ai nashi wasa ne.

Yanada da kyau wadannan furodososhi da Selebiriti su fahimci cewa idan matan da suke bautar da su na yanzu sun kasa fitowa fili su bara ko su kai kara gaban kuliya, akwana a tashi za a iya samun wata ko wasu da bazasu hakura da wannan yaudaran da bautar cin zarafin da yanzu haka wasu suke fuskanta.
Don haka ya dace suyi abunda har bayan ransu bazasu fuskanci abun kunya da kaskanci irin na wannan mawakin wanda ya shahara, yayi fice ga magoya birjim a duk duniya ga kudi a jimge, ya yi zaton bazai tabu ba, yayi tunanin ya ci banza sai ga shi ya barke da kuka ganin ya shiga hannun manta sabo.

Banyi tunanin a duk furodusoshi da Selebiriti da muke da su a masana’antar mu ta harkar fim da Waka ba akwai wanda yake da rabin abin da K Kelly ya ke da shi na daukaka ba.
Wannan ya kamata ya zama izzina da darasi ga dukkanin mu bama su Selebiriti ba. Domin sharri dai takan komawa kan mai yinta ne. Da fatan Allah Zai taimaka mana wajen kare kanmu daga fadawa jin kunyar duniya da lahira.

©Tonga Abdul Tonga

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button