Ƴan bindiga sun kai wani ƙazamin hari wanda yayi sanadiyar rasuwar rayuka da yawa a kastina


Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe Mai gari da ɗansa da wasu mutune taƙwas a kauyen Kukar Babangida da ke Karamar Hukumar Jibia a Jihar Katsina.
Kamar yadda Katsina Reporters ta samu, a daren ranar Laraba ne ’yan bindigar suka yi wa mutanen ki-san gilla, ciki har wani mai gadi da suka yi wa yan-kan rago.
Wani dan yankin da ya nemi a boye sunansa ya ce, zugar ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 10 na dare, inda “suka ka-she mai gari Magaji Haruna da dansa Idris, tare da wasu mutane uku a gidansa.
“Sun kuma shiga wani kamfani mai suna Tinna Tech inda suka yi wa wani mai gadi yan-kan rago, dayan kuma suka harbe shi har lahira, sannan suka cinna wa manyan motoci biyu da wata karama wuta.”
Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun yi awon gaba da mata dama, amma ba a kai ga tantance adadinsu ba, kamar yadda Aminiya suka ruwaito.
Shaidan ya ce tun da misalin karfe 5 na yammacin ranar aka fara fargabar yiwuwar kawo hari, sakamakon ganin ’yan ta’adda a kusa da kauyukna Taka-Tsaba da Yargeza.
Ya ce, saboda haka aka sanar da jami’an tsaro abin da ke faruwa, amma kuma a karshe da ’yan bindigar suka kawo farmakin babu wani mataki da suka dauka na dakile harin.
“Duk da cewa jami’an tsaro sun ba mu tabbacin cewa akwai karin jami’ai da za su turo idan har akwai barazanar hari, amma haka ’yan bindigar suka zo suka shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka, jami’an tsaro sun zo ba.
“Sai da ’yan bindigar suka gama barnarsu suka tafi sannan wata motar jami’an tsaro kwaya daya ta zo,” in ji shi.
Mazauna yankunan dai na zargin gaggan jagororin ’yan ta’adda Dankarami da Dangote ne ke aiwatar da hare-haren da ake fama da su a Karamar Hukumar Jibia da kewaye.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





