Gobe Juma’a kotu zata yanke hukuncin zaɓen jihar kano


Kotun daukaka kara ta sanya Juma’a, 17 ga watan Nuwamba, a matsayin ranar yanke hukunci kan karar da gwamnan Kano ya daukaka inda yake kalubalantar soke nasarar zabensa.
Abba Kabir Yusuf ya garzaya gaban kotun daukaka kara ne bayan kotun korafin zabe ta jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba, ta rushe nasarar da ya samu, inda ta ce abokin takararsa na jam’iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna ne halastaccen wanda ya ci zabe. 

majiyarmu ta BBCHausa na ruwaito Kotun dai ta kafa hujjar hukuncin da ta yanke ne a kan kuri’a 165,… da ta soke daga cikin abin da Abba Kabir Yusuf na NNPP ya samu, saboda rashin sa hannu da kwanan wata da kuma hatimin hukumar zabe. Jam’iyyar APC dai ta roki kotun ta yi watsi da karar da Gwamna Abba Kabir ya daukaka.
Hukuncin kotun daukaka karar na zuwa ne kwana goma cif bayan alkalan kotun da ke zama a Abuja, sun saurari bahasin dukkan bangarorin da ke cikin shari’ar, tare da sanya hukuncinsu a mala, sannan suka ce za su sanar da ranar yanke hukunci nan gaba
Wata takardar kotun daukaka kara da BBC ta gani, ta lissafa APC da NNPP da kuma INEC a matsayin wadanda ake kara. Sannan ta ce kotun za ta fara zaman yanke hukunci daga misalin karfe 9:00 na safe
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




