Wani matshi yayi tattaki daga kasar chadi zuwa Nigeria domin yaga rarara


Mai taimakawa Dauda Kahutu Rarara a kafafen sada zumunta ya wallafa wani gajaren bidiyo na wani masoyin rarara da yayo tattaki daga ƙasar chadi zuwa ƙasar Nigeria domin yaga rarara.
An zanta da wannan masoyin rarara inda ya kawo dalilin yin wannan tattaki da yayi daga kasar domin zuwa Nigeria .
Ga abinda yake cewa:
“Sunana musa isiyaku nazo daga kasar chadi domin inga masoyina mawaki rarara gaskiya tasowa naga chadi zuwa nan na fuskanci ƙalubali daban daban a rayuwa idan anka zo a inda ma’aikata za’a tambayeni takardu idan babu za’a ce sai na biya 1500 babu adadi da na kashe domin shigowa Nigeria.
Burina kawai nazo naga rarara kawai abinda bukata naga rarara naje kano ina tambaya aka kaini zoo road akace a’a katsina zakaje jiya da dare na hau mota shine da inaso nayi bayyani shine anka kawo ni inda wannan mutane.
Nayi musu bayyani nifa kawai nazo naga masoyina rarara saboda irin kaunar da nake masa Allah kawai yasan irin son da nake masa dare da rana ina saurarin wakokinsa da nake ya zamomin karatu ko bacin rai nake dana saurari wakokinsa shikenan nakanji salama yana saukomin.”
Martanin mutane akan wannan bidiyo da munka tattaro.
@Sule Gehe cewa yake :
Him Allah Karabamu Da Mutuwar Zuciya Wallahi Yakamata Matasa Mugane Idan Munason Mutum Bawai Tattaki Daga Wani Gari Ko Wata Kasa Shikesawa Agane Kai Masoyinsa Bane Indai Soyayyar Da Kakeyimai Ta Gaskiyace To Ah Inda Kakema Kayimasa Addu,ah Ta Wadatar Amma Wai Saboda Hauka Da Nemanma Kai Wahala Bakayi Tattaki Akan Addinin Allah Ba Sai Wani Allah Yasa Mudace
@Mubarak haruna Muhammad yana cewa :
Wlh masoyi ne na gaske dan ni nayi fira da shi na tabbatar duba da yanda na fahimce shi hata wadan da suka ce suna san chairman Rarara a lokacin yaji dadin ganin su
@mubarak ibraheem kaita cewa yake :
Wahalu kawai wannan Abun gskia mutane basuyi ma kansu adalci kawai ka fasko hanya Dan wani kawai dai wani salon Neman kudi ne kawai.
@Sadi Muhammad cewa yake:
amma kacika mahaukaci shi raran sai kace sahabi tindaga chadi kazo a kafa lalle akwai mahaukata a duniya Allah yabaka lafiya.
@UMAR YOBE RARA 001 cewa yake:
gaskiyane Allah yakarawa Chiyaman dauda adamu abdullahi kahutu rara Allah yakarawa Chiyaman masoya na gari.
@saadualiyu869 cewa yake:
kaji dan wahala Allah yakara maka wahala duniya da lahira wawa jaki shege Mai kai uwa kwallon mango
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






