Labarai
An Daga Taron Maulidin Nyass A sokoto Saboda Coronavirus – Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Advertisment
Shugaban Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sanar da cewa an dage taron Maulidin Sheikh Nyass wanda da za a yi a Abuja da Sokoto saboda yaduwar cutar coronavirus.
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce saboda yadda cutar ke yaduwa a makwabtan Najeriya, kuma taron maulidin ba na ‘yan Najeriya ba ne kawai, har da ma ‘yan wasu kasashe.
Ya ce ba za a yi taron ba har sai annobar ta lafa a duniya sannan a sanar da ranar da za a gudanar da taron.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com