Labarai

Yadda yarinya yar shekara 13 take sana’ar sayar da Aya ba take samun Naira 120,000 a wata

Sana'a ba sai gwamnati ta koya maka ko an baka jari ba - Dr. Sheriff Almuhajir

A yau din nan dr sheriff Almuhajir ya bada labari mai ban mamaki da hikima a cikinsa wanda ya wallafa a shafinsa inda labarin ya burge mutane matuka sosai.

Sana'a ba sai gwamnati ta koya maka ko an baka jari ba - Dr. Sheriff Almuhajir
Dr.sheriff Almuhajir

Na irin yadda karamar yarinya mai shekaru 13 take sana’a wanda kuma take samun kudi zunzurutu wanda babu wani babban jari amma idan ka lissafa zaku fahimci tafi wasu ma’aikatan gwamnati sosai albashi.
Dr Sheriff Almuhajir ya bada labarin ne. A yau din nan a shafinsa na sada zumunta.

Yanzunnan na tsayar da wata yarinya mai kimanin shekaru 13, tana sayar da ayaba, bayan na sayi ta 2,000, sai na tambaye ta.

Yarinya ayabar nawa kika sayar yau? Ta ce ta N8,000, na ce; tana kila dauko, ta ce; na dauko ta N4,000. Nace; yaushe kika fito, tace; bayan na dawo daga makaranta “kamar 2:30 kenan”.

Yanzu kun ga wannan yarinya mau shekaru 13 mai jarin N4,000 ta ci ribar 4,000 daily, in 30 days za ta iya samun N120,000, wato 100% return on investment. Wannan Yarinyar tana samun abunda matasa biyu ma su degree a Damaturu ba sa samu.

Ina fata kun gane sana’ah ba sai Gomnati ta koya maka sana’ah ba, shin kun gane ba sai an baka jari ba. Girman kai kawai ake cirewa a samu kudi, ko kuma a dauko waya ana ta dannawa.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button