Aminu J Town yayi martani mai Zafi kan kalaman Kalaman Ahmad Lawal da Sunkayi Muni kan musulunci


Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood lawan Ahmad jarumin cikin shirin izzar so ya bayyana wasu abubuwa da suke cikin shirin izzar so a cikin hirar da jarumar Kannywood Hadiza Gabon tayi dashi.
A cikin tattaunawar da akayi da Jarumin Lawan Ahmad akwai wata tambaya wadda ta burge wasu ta kuma matawa wasu rai inda yake cewa Duk wanda yakeso a gama shirin izzar so baya kishin musulunci.
Dalilan da yasa Lawan Ahmad ya fadi wannan kuwa shine akwai mutanen da suka karbi addinin musulunci ta dalilin kallan wannan shirin dan haka lallai shirin ba karamin sako yake isarwa ba dan haka babau yadda za ai a gaba wannan shirin na izzar so
Kamar de yadda kuka sani Aminu J Town mawaki a kannywood a kwanakin baya ya dinga sakin bidiyoyi a dandalin tiktok tare da tona asirin abinda ke faruwa a cikin masana’antar Kannywood wanda a lokacin wasu sun mayar mishi da martani wasu basu mayarba don haka dan yayi wannan martanin zuwa abinda Lawan Ahmad ya fada ba wani abin mamaki bane.





