Labarai

Kwankwaso Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Advertisment

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga jam’yyar PDP.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da tsohon gwamnan ya sanya wa hannu a ranar talaga Aminiya trust na ruwaito.
Idan ba a manta ba, Sanata Kwankwaso ya jima yana shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar, tun bayan kafa tafiyar siyasa ta TNM.
A ranar Lahadi ce, daya daga cikin jagororin darikar Kwankwasiyya kuma na gaban goshin Kwankwaso, Injiniya Abba Kabir Yusif (Abba Gida-gida), ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP, mai alamar kayan marmari.
Abba Gida-gida dai ya zargi jam’iyyar PDP da gaza bai wa bangaren na Kwankwasiyya dama, duk da irin halarcin da su kai wa jam’iyyar a zaben 2019.
Ana sa ran Kwankwaso zai tsaya takarar Shugaban Kasa a inuwar jam’iyyar NNPP, a babban zaben 2023 da ke karatowa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button