Labarai

Buhari da Gwamnatin sa sun Gaza Akan Harkar Tsaro – Salihu Tanko Yakasai



A jiya ne bomb ya tashi da jirgin kasa wanda ke make da fasinjoji a ciki daga Abuja zuwa Kaduna, inda yan bindiga suka tashi bomb din, kuma suka budewa jirgin wuta har suka kashe wasu, wasu kuma suka ji ciwo.
Wannan na zuwa ne kwana kadan bayan da yan bindiga suka kai hari filin jirgin sama a Kaduna. A wannan harin shi ma anyi musayar wuta da su da jami’an tsaro. Da ma ai an ci gaba da kashe mutane a Zamfara da Katsina.
Kaga kenan daina bin titi da manyan jami’an gwamnati suka yi, saboda gudun yan bindiga, suka koma bin jirgin sama da jirgin kasa, gashi nan abin ya fara zuwa kan su suma. Haka matsala take, idan ba kai maganin ta ba saboda kai kana da yadda za kayi, a kwana a tashi sai wataran ta zo kan ka. An kyale talakawa da baza su iya bin jirgin kasa ba ana ta kai musu hari akan titi, toh gashi abin ya zo kan jirgin kasa.
Kullum yan gwamnatin Buhari zancen su baya wuce a ce mana ana manyan aiyuka kamar su titina da gada da jirgin kasa. Idan har baza a iya kare rai da dukiyoyin mu ba, toh meye amfanin wannan aiyukan da ake kururuwar ana yi?
Rashin gina al’umma a baya shi ya kawo mu cikin wannan yanayi a yau, haka zalika idan ba’a gina al’ummar yau ba, Allah ne kadai ya san irin halin da zamu tsinci kan mu a gobe.
Haka kuma kullum idan matsalar tsaro ta tabarbare, mutane sukayi caaa akan gwamnati, sai kaga gwamnati ta dan yi yunkuri an tashi tsaye kamar gaske, amma da an kwana biyu Alaji sai kaga an saki jiki, sai tsaro ya sake tabarbarewa. Ya zama wajibi a tsaya tsayin daka ayi maganin matsalar tsaro, ko kuma abin yai yawa, wai mutuwa ta shiga kasuwa.
Ina mika taaziya ta ga iyalan wadanda suka rasa ran su, Allah jikan su da rahama Ya baku hakurkin jure rashin. Wadanda kuma aka harba ciki harda Mohd Zameen wani kani a waje na daga Kaduna, ku kuma Allah baku lafiya Ya bi muku hakkin ku. Allah kuma Ya ci gaba da kare mu, sannan Ya kawo mana karshen wannan masifar amin.
Salihu Tanko Yakasai (Dawisun Kano)
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button