Zan jagoranci zanga-zangar fatattakar Pantami daga kujerar minista a Najeriya, In ji Aisha Yesufu
Shahararriyar ƴar gwagwarmayar nan yar arewa mai zama a legas, ta saki wani sabon faifan bidiyo da take nuna cewar, itafa a shirye take domin shiga gaba domin a tsige ministan sadarwa na ƙasa Dr. Isah Ali Pantami.
A Bidiyon da fitacciyar ‘yar gwagwarmayar Aisha Yesufu ta fitar kuma yake yawo a shafukan yanar gizo, ta ce
“Ni da kai na zan jagoranci zanga-zangar da ba a taba yi ba a Najeriya, har sai Isah Pantami ya sauka daga kujerar minista a kasar nan.“
Kamar yadda jaridar mikiya na ruwaito.Ministan sadarwa na ƙasa, Dr Isah Ali Pantami ana masa zargin cewa yana da alaƙa da ƙungiyar ƴan ta’adda ta Alƙaida ne, zargin daya fito ya musanta kuma yace koda yayi zancen yayine a bisa kuriciya.
Ko ita ma gwamnatin tarayya, ta fito ta wanke shi suɓul da sabulu mai kamshi.
To amma duk da wannan batu, Aisha Yesufu tana nan akan bakanta, tare da sauran mazauna kudancin Najeriya da dama.
Idan za’a iya tunawa, A’isha Yesufu tayi ƙaurin suna ne wajen jagorantar yin tirjiya ga gwamnatin tarayya a wani lokacin harda ta jihohi, wanda a cewar ta neman ƴanci takeyi.
Zanga zangar #Endsars itace ta ƙara sawa tayi ƙaurin suna, amma kafin nan, ta shahara sosai wajen tafiyar nan ta Bringbackourgirls.
To sai dai ba kasafai aka cika ganinta ta fito tana goyawa arewacin Najeriya baya ba, yankin da ake ganin daga nan ta fito.
Yanzu abin jira agani da shine, shin da wani mataki zata jagoranci tafiyar ganin Pantamin yakai ƙasa? Lokaci ne kawai zai iya nunawa!
Kada ku sake ce mata yan gwagwarmaya illah ya tayar da tozarma