Rashin kirkirar sabbin masarautu a Kano shi Ya fi alkhairi – Sheikh Daurawa
Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Daurawa ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin mutanen jihar
– Daurawa ya ce, a tunaninsu barin kirkirar sabbin masarautun nan a jihar Kano zai fi zama alheri,jaridar legithausa.ng ta ruwaito.
– A ranar Alhamis ne majalisar jihar Kano din ta amince da kirkirar sabbin masarautun
Sanannen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin mutanen jihar kafin kirkirar sabbin masarautun.
A tattaunawar da Shehin malamin ya yi da Hausa RFI, ya ce suna ganin rashin kirkirar sabbin masarautun shi zai fi alheri, don kauce wa wargaza kawunan al’umma.
Sai dai kash! A ranar Alhamis ne majalisar jihar Kano din ta amince da dokar kirkirar sabbin masarautun. Hakan ya biyo bayan gabatar da kudirin da Ganduje ya kara yi a gaban majalisar a ranar Litinin da ta gabata.
Bayan an karanta bukatar kashi na uku a ranar Alhamis, majalisar ta amince da hakan ya zamo doka a jihar. Duk kuwa da cewa babbar kotun jihar ta soke sabbin masarautun tare da dakatar da sarakunan da gwamnan ya nada.
Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin, Labaran Abdul-Madari ya ce, manufar kirkirar sabbin masarautun, ita ce bunkasa ci gaba a fadin jihar kuma sun dau matakin domin talakawa ne.
A shekarar da ta gabata ne, Gwamna Ganduje ya kirkiro da sabbin masarautun, lamarin da ya ja ake kallon za a rage karsashin Mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.
Sabbin masarautun sune: Bichi, karkashin Aminu Bayero; Rano, karkashin Tafida Abubakar-Ila; Karaye, karkashin Ibrahim Abubakar sai kuma Gaya, karkashin Ibrahim Abdulkadir.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





