Film Din “Barayin Zamani” Ya kawo Barna maimakon Gyara.
A jahar sokoto a unguwar rogo an damfari wata mata da rago inda aka tafi da yaranta 3.
A ranar 15 ga wannan na Ramadan da muke cikin ne wani dan damfara kuma matsafi ya yaudari wata mata a unguwar rogo a nan cikin birni sokoto inda yazo da rago jaye a hannu har gidan wata baiwar Allah mai suna Aisha,ita dai Aisha mijinta ya kasance dan kasuwa ne Wanda haka yasa bai zama gida wanda kuma shine ya baiwa wannan dan damfara damar damfarar Aisha ya’yanta har 3. Shi dai wannan dan damfara yazo ne da rago rike a hannu inda yace mai gidanta ne ya sayo shi yace a kawo gida,bayan haka kuma yace azo da yaransa 3 don aje a gwada su dinkin sallah da za a misu wanda ganin haka yasa sai Aisha ta amince ta bashi wadannan yara har 3. Bayan dan wani lokaci ne taga yaranta basu dawo ba kunsan uwa da ya’yanta bata iya jurewa na tsawon lokaci bata gansu ba shine sai ta kira mijinta ta tambaye shi wai har yanzu ba a kare gwada su bane? To a nan fa mijinta nata ya shaida mata cewa shi bai aiko wani da rago ba ballantana wani dinkin sallah” sannan saninki ne duk sallah ba sai an gwada su ba ake misu dinki ba” yanzu haka dai Allah yawa Aisha cikawa bayan taji cewa sace ya’yanta ne akayi. Allah yajikanta da rahama.
Sharhi: a cikin film din “Barayin Zamani” an nuna yanda ake irin wannan damfara inda sulaiman bosho yazo da kayan miya yace mai gida ne ya aiko shi sannan yace a bada generator a masa service. Haka shima Ayatullah Tage yayi yunkurin irin wannan damfara duk a cikin film barayin zamani. Sadeeq Sani Sadeeq shima ya nuna yanda ake irin wannan damfara.
Shawara: a gaskiya yan film yakamata kusan irin film dinda kuke shiryawa domin mugayen mutane suna amfani da wani abu daga cikin FINA finanku suna yaudaran jama’a kamar film din BARAUNIYA wannan film ya koyawa mata yanda ake sata.
Yanzu haka dai Aisha ta rasa ya’yanta ta rasa ranta,mijinta kuma yana kwance asibitin kwararrun a nan cikin birnin sokoto wata Specialist Hospital sokoto. Allah ya bashi lafiya ya kuma bayyana wadannan yara idan suna raye.
Daga:Comrd S-bin Abdallah Dandege