Labarai

An Sace Kudin Sadaki Ana Tsaka Da Daurin Aure A Kano

Advertisment

Wani abun kamar a fim amma kuma ace zahiri ne tabbas wannan labarin akwai nishadantarwa sosai a cikin amma kuma wanda ya wallafa labarin dan zaria ne ko dai barkwancin da ke tsakanin kanawa da bazazzage ne sunka tashi. Kamar yadda wani shafi mai suna Daily News Hausa sunka ruwaito a facebook suna cewa.An Sace Kudin Sadaki Ana Tsaka Da Daurin Aure A Kano

“A jiya laraba ne 16/03/2022 akaje daura aure daga garin Igabi na jihar Kaduna, zuwa Kano kamar yadda rahotonnu ke tabbatar mana da hakan, “Inda aka nemi sadaki sama ko kasa ba’a Ganshiba.

Sakamakon hakan yasa aka bata lokaci ba’a daura auren ba ana ta kallon kallo a tsakanin juna, Amma daga bisani aka gani a cikin babban rigan daya daga cikin waliyan amarya, inda yace shi bai ma San yadda akayi kudin suka zo jikinshi ba anan dai aka kori waliyin zuwa waje. Inda aka Kira kanin shi da yazama cikon waliyyan amaryan.

Wannan lamari ya farune a kano a wata unguwa da ake kira da kurna.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button