Mahaifinsa yana buƙatar ƙara aure amma ba shi da kuɗi, ya umarce shi ya ɗau nauyin auren, mahaifiyarsa tace idan ya ɗauka zata tsine min Albarka? – Dr. Bashir Aliyu Umar
Tambaya
Assalamu alaikum warahamatullah malam mahaifina ya sanarda ni yana da bukatar ƙara aure, yana da ragowar sha’awa ya buƙaci na dauki nauyin aurensa tabbas Allah ya horemin zan iya hakan domin ceto mahaifina daga hallaka.
Amma yan uwana suna fushi dani kuma mahaifiyata tace idan na bawa mahaifina gudumuwa yayi aure zata tsine min albarka malam dan Allah ya zanyi.?
Amsa
Wato wajibi ne ga ɗa idan mahaifinsa yana da bukatar ya dauki nauyin Mahaifinsa daga cikin bukatar mahaifinsa wato ya dauki nauyin matarsa idan mace daya yake da ita bazata iya katange shi ba,ma’ana bazata iya katange daga shiga sha’awa ta haramun ba.
To dole ne ɗan ya dauki nauyi yi masa aure da nauyin matar wannan wajibi ne da Allah ya ɗora masa.
Amma yan uwansa da ke fushi da shi yana yiyuwa mata ne,idan akwai maza ya kamata su fahimci sha’ani da alaƙar aure, amma daman su mata kar ka damu zasu taya mahaifiyarsu fushi.Daman ita mahaifiya zatayi wanann kuma bai kamata ka gayamawa mahaifiyar ba.
Sai ka bashi gudumuwar koda bata sani ba ma’ana asirance.
“Sa’a nan idan ta sani tace zata tsine maka, tsinuwar bazata bika ba.”
A cikin fatawar malam ya kawo wata kisa inda yace akwai wani bawan Allah wanda suke kauna walin Allah ne, inda akwai darasi sosai cikin wannan kisar yana da kyau kowa ya saurara yaji.
Ga bidiyon kasa ku saurara.


