Addini

Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilinta na kwashe Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi



Shugaban hukumar kula da ababan hawa da muhalli ta jihar Kaduna, KASTELEA wato Manjo Garba Yahaya Rimi, kuma shugaban kwamitin yaƙi da annobar korona a jihar ya bayyana cewa kai samamen na daga cikin matakan da suka fara ɗauka na daƙile annobar korona.
A ranar Laraba ne gamayyar jami’an tsaro suka kutsa cikin gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe duka almajiran da ke kwance a tsakar gidan.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce wannan matakin ba wai ya tsaya bane kan makarantar Dahiru Bauchi kaɗai, inda ya ce ya shafi duka ƙananan hukumomi 23 ne na jihar.
Kamar yadda BBCHAUSA na ruwaito.Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa ɗalibai 140 suka kwasa daga makarantar kuma an ajiye su sansanin alhazai na jihar Kaduna inda ake tantance su, inda ya ce akwai wasu daga cikin almajiran da suka fito daga ƙasashe kamar Nijar da Chadi.
Gwamnatin ta ce idan aka gama tantance almajiran, waɗanda suka fito daga wasu jihohi za a miƙa su ga gwamnonin jihohinsu, na jihar Kaduna kuma za a miƙa su ga ciyamomi na ƙanan hukumomi, ɗaliban ƙasar waje kuma za a miƙa su ga hukumar shige da fice ta Najeriya.
Ko a bara sai da gwamnatin jihar ta mayar da wasu almajirai garuruwansu, inda ta zarge su da yaɗa korona.









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button