Yanzu-Yanzu: Buhari Ya amince a Bude Masallatai, majami’u Da kasuwanni A fadin Tarayya
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarar kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19 PTF na sassauta dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar.
Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da cewa an sun gana da shugaba Buhari kuma sun bashi shawara kan matakin da za’a dauka gaba.
Bayan ganawar, Shugaban kasa ya amince da bude wuraren Ibada (Masallatai da Majami’u kadai) da kasuwanni a fadin tarayya amma da sharadin za a bi dokokin da hukumar NCDC ta gindaya.
Yace: “PTF ta mika shawarinta kuma shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a aiwatar da su cikin makonni hudu masu zuwa fari daga ranar 2 zuwa 29 ga watan Yuni, 2020.”
“An sassauta dokar hana taruwa a wuraren Ibada bisa ga sharudan da PTF ta gindaya da kuma yardar gwamnatocin jihohi.”
“Za’a amince a rika shiga kasuwanni da wuraren tattalin arziki amma da lura saboda takaita yaduwar.”
SGF:iv. Sustenance of key non-pharmaceutical interventions that would apply nationwide and include:
a) Ban of gatherings of more than 20 people outside of a workplace;#PTFCOVID19
— Covid-19 Presidential Task Force (PTF) | Nigeria (@DigiCommsNG) June 1, 2020
A bangare guda, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Shugaban kasa ya amince da sassauta dokar hana fita a jihar Kano.
A hirar kwamitin da manema labarai ranar Litinin, 1 ga Yuni, Boss Mustapha, ya sanar da hakan ga daukacin mutan jihar Kano.
Yace: “An sassauta dokar hana fita a jihar Kano.”
“Za’a cigaba da taimakawa gwamnatocin jihar wajen tabbatar da cewa su zasu cigaba da gudanar da aikin aiwatar da shawari da dokokin da kwamitin PTF ta gindaya.”
“Hukumar NCDC za ta cigaba da baiwa jihohi gudunmuwa ta hanyar basu shawari musamman kananan hukumomin da aiki yayi yawa.”

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






