Kannywood

AKAN MUTUWAR BABAN ALI NUHU: Ba Daidai Ba Ne Musulmi Ya Yi Murna Da Mutuwar Wanda Ba Musulmi Ba ~ Indabawa Aliyu Imam

Advertisment

Daga Indabawa Aliyu Imam

Ba daidai bane musulmi ya yi murnar mutuwar wanda ba musulmi ba, domin samun kanka musulmi kai ma ba wayonka, ba kuma ka san yadda karshen ka zai kasance ba.

Amma kuskure ne maigirma a dinga kwatanta mutum irin Ali Nuhu da Annabawan Allah, naji wasu na cewa ai Baffan Annabi ma ba’a kan musulunci ya mutu ba, ko matar Annabi Ludu da matar Annabi Nuhu da d’ansa mushrikai ne, wai don haka ba wani abu bane a kan Ali Nuhu.

Tabbas hakan ba aibu bane ga Ali Nuhu, mu kanmu ba mu ji dadi ba, mun tausaya masa, kuma jiya munyi masa ta’aziyya, mun bashi hakuri, har  addu’a mu kayi cewa damu da Ali Nuhun Allah ya sa mu mutu muna musulmi, domin ba mu san kaddararmu ba.

Duk da yake na yabi Marigayi Nuhu Paloma cewa an ce mutumin kirki ne mai haba-haba da jama’a, na kuma yi wa d’ansa Ali Nuhu ta’aziyya duk da cewar kun san halinsa, amma wasu suna suka ta wai naci masa fuska, shin mutum irin Ali Nuhu mai rawa da ‘yan matan mutane, mai saka ‘ya’yan mutane a harkar film ta lalata tarbiyya har  yana da fuskar da za’a ci masa ne? Shekara nawa ya dauka yana lalata musulunci da tarbiyar al’umma?  Shekara nawa ya dauka yana saka ‘yan mata cikin mummunar harka? kawai daga ta’aziyya sai cibi ya zama kari? Karamci sai ya zama cin fuska?

Masu ganin aibun carman dudu da d’an maliyo-maliyo da muka ce a karantawa Nuhu Paloma basu kyauta min ba, wannan ba wani abun aibu bane a al’adar garinmu Kano ba, wannan ita ce addu’ar da musulmi ke wa wanda ba musulmi ba a yayin ta’aziyya, Allah ya ji kan ‘Dan masanin Kano yayi irin wannan addu’a a ta’aziyyar tsohon gwamnan Kano na lokacin soja, sarkin Kano Ado Bayero ne ya ce a yi hakan, kuma babu wanda ya ce bai kyauta ba, domin mu dai addininmu ya hane mu addu’a wa kafirin da ya mutu, amma bai hana mu yi musu ta’aziyya ba, mene laifina don na kwaikwayi magabatana ? kenan idan bance ayi carman dudu ba, Allah ya kara nauyin kasa kuke so na ce? Ni ba zan fadi haka ba, bai kamata ba. Amma carman dudu Allah ya sani da kyakkyawar niyyar ta’aziyya nace ayi ba da wata niyya ba. Ni dai na san ban fadi wata magana mara dadi a kan mutuwar baban Ali Nuhu ba, balle ace ban kyauta ba.

Hallau muna ta’aziyya ga Ali Nuhu Paloma Allah ya bashi hakuri, mu da shi Allah ya sa mu mutu a musulunci, muna addu’a Allah ya shiryi Ali nuhu ya ji kan Mahaifiyarsa Hajiya Fatima cikakkiyar musulmar jihar Borno.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button