Kannywood

Tun Ina Karama Nake Sha’awar Yin Fim, Shi Ya Sa Na Yi Digirina A Kansa, Cewar Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi tana cikin jaruma ce wadda take da dinbin hazaka da fasahar a duk lokacin da take gudanar da shirin fim. Tana iya fashewa da kuka da hawaye duk lokacin da ta ga dama. Nafisa Abdullahi wadda ake yi wa lakabi da Kazar Hausa ko ‘Ya Daga Allah tana da digirin a bangaren aikin fim da ta kammala a jami’ar Jos kuma tana karatun digiri na biyu a wata jami’ar kasar Burtaniya kan daukar hoto.
Kamar yadda arewablog na ruwaito,An haife ni a garin Jos, na yi makarantar firamare da jami’a duk a garin jos, inda na karanci harkar fina-finai a digirina na farko. Jarumi Ali Nuhu shi ne wanda ya yi salar shigata harkar fim ta Kannywood har na kawo matakin da nike yanzu. Fim dina na farko a masana’antar fina-finai Kannywood shi ne (Sai Wata Rana)
Da aka tambaye ta ina maganar soyayyar su ta kwana da shahararren jarumi kuma mawaki Adam A. Zango ta kwana? Sai ta kada baki ta ce kusan shekara hudu zuwa biyar da da rabuwa. Idan mun hadu ana gaisawa, amma ba mu cika haduwa ba. Kuma duk fim din da ka ga na fito a ciki sai na karanta labarin in na ga ya kwanta mi zan yi shi. Da gaske ina da baiwar duk sadda na ga damar yin kuka a cikin fim zan iya yin sa.
Muna zaman lafiya da sauran jarumai maza da mata, babu wadda muke zaman doya da manja, duk da ana samun sabanin yau da kullum, amma kusan ina shiri da kowa a wannan katafariyar masana’antar kannywood ta mu. Wasu na kallon jaruma Nafisa Abullahi ‘yar girman kai da wulakanta masoyanta, inda ta ce gaskiya ba haka ba ne, sai dai ina da dabi’ar ta rashin yin Magana kuma ban wulakanta dan Adam ba halina ba ne.
Ta bayyana dalilin da ya sa aka rage ganinta a cikin fina-finai a yan kwanakin nan, inda ta ce ayyuka ne suka yi man, ba na fim ba kawai, akwai huddudin da yawa da nake yi, kuma ba kowane fim nake karba ba. Amma yanzu haka ina shirya fim nawa na kaina wanda zai fito kwanan nan insha Allah. Na taba yin fim din turanci a jihar Bauchi, tun kafin na fara shiga na Kannywood, inda a wajen daukar fim din muka gamu da jarumi Ali Nuhu ya yi man alkawarin zai sanya ni fim din Hausa, kuma ya fara sanya ni a fim din (Sai Wata Rana) kuma har gobe shine ubangidana na farko a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu Ogana ne yana da matsayi sosai a wurina.
Da aka yi mata maganar ko yaushe za ta yi aure? Inda ta amsa cewa aure lokaci ne, amma ina da niyyar a raina. Insha Allah zuwa shekara mai zuwa ko ta sama saboda lokacin kawai nake jira. Babbar kawata ita ce jaruma Halima Atete kusan tamu tafi zuwa daya. Amma na fi abotaka da maza, mafi yawan aminaina maza sun fi yawa kamar su Zaharadeen Sani da Nura M. Shareef da sauransu.
Rashin mahaifiyata a watanni baya, shi ne abinda ya fi girgiza ni a rayuwata, saboda it a ce jigon rayuwata ko rayuwarmu mu biyar da ta Haifa. Mahaifinmu tun muna kanana ya rasu ita ce ta dauki dawainiyar rayuwarmu ta hada zumunci sosai, ta nuna mana kauna sosai, Allah ya jikanta da rahama.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button