Labarai

CORONA: A Karshe Gwamna Elrufai Ya Janye Dokar Hana Zirga-zirga A Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya sassauta dokar kulle da ya sanya a faɗin jihar Kaduna domin dakile yaduwar cutar corona virus.

El-Rufa’i ya yi umarni da a buɗe masallatai da majami’ai domin gudanar da sallar Juma’a da Ibadun ranar Lahadi ga kiristoci.

Haka zalika ya yi umarni a buɗe manyan kanti da wasu bangaren kasuwanci amma banda kasuwanni da makarantu.

Suma ma’aikata za su koma bakin aiki, yayin da ‘yan Jaridu da sauran jami’an tsaro za su ci gaba da aiyukansu kamar yadda aka saba.

Ya kuma baiwa ‘yan sufuri dama su ma su ci gaba amma mutum biyu kawai za a rika ɗauka a kowani layin kujerun mota. Ga ƴan Bus kuma, an amince da su ɗauki kaso hamsin na mutane da motar su ke dauka.

Za a ci gaba da gudanar da harkoki a Kaduna ne kawai daga karfe 8 na safe zuwa 6 na yamma.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button