Kannywood

Tabarar da mata masu yabon ma’aiki ke yi ta zarce ta masu rawar TikTok da ‘yan fim, Fantimoti

Fitacciyar mawakiyar finafinai a baya, yanzu haka kuma sha’ira a fannin yabon manzon Allah SAW, Maryam Fantimoti ta ce tabarar da mata sha’irai masu yabon ma’aiki su ke yi, ta fi ta ‘yan rawar TikTok da ‘yan fim.

Kamar yadda ta shaida wa Freedom Radio Kano, ta ce dangane da shigarsu ta fitar da surarsu, cakudewa tsakanin maza da mata da suke yi ya munana.Tabarar da mata masu yabon ma’aiki ke yi ta zarce ta masu rawar TikTok da ‘yan fim, Fantimoti

A cewarta:

Abinda yasa nayi magana akan na hadarar manzon Allah SAW shi ne yadda ake yawan korafi akan yabon manzon Allah a gyara. Na daya a gyara alkaluma. Na biyu a gyara harshe, sannan a gyara dabi’a ta sha’irai.

Saboda mu mata ne. Wata sha’irar idan ki ka kalleta sa’ar ‘yar da na haifa ce. Za ki samu ta yi shiga irin ta su ta yara.

Ya kamata a gyara. Ina ganin kuma duk abinda ake yi yayin yabon manzon Allah SAW in dai ya saba wa dabi’a to ina tunanin wannan abin ya yi muni.

A bangaren wata sha’irar ta ce sam ba haka bane. Bai dace a yi wa sha’irai kudin goro ba.

Batun shiga ce, yanayin waka da cakuduwa tsakanin maza da mata. Kuma hukumar tace finafinai tana iyakar kokarinta wurin tantance wakoki tare da tace su.

Ta ce yanzu haka dai an dena samun irin wadannan matsalolin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button