‘Yan Film Kunci Amanar Talakawa Da Masoyanku Sakon Jaruma Rahama Hassan Ga ‘Yan Film
Wannan wani sako ne da jaruma rahama hassan ta wallafa a shafinta na sada zumunta wato facebook irin yadda sunkayi tallar jam’iyyar apc ta mai girma shugaba Muhammadu Buhari.
Ga abinda tace.
“Gareku Yan Kanywood da duk wasu mashhuren Mutanen da suka taya Jam’iyar Apc Tallata Mai Girma Shugaban Kasa na neman takara zango na biyu karkashin Taken NEXT LEVEL
Kunyi amfani da Soyayar da talakawan wannan kasa suke muku kuka saka su suka sake zabe Mai girma Buhari, kuma sun amsa sun zabe shi,
To in har da Gaske kunyi hakane don Son ganin anyi gyara a wanann kasa ne to yana da kyau ku fito ku sanar da Mai girma Shugaban Kasa Halin da Talaka yake ciki na rashin tsaro da yake fama dashi a wannan kasar ,
ku masa kira ta shafukanku da kuka tayasa yakin neman zabensa
Domin wallahi akwai Kauyuka da yawa da basu iya bacci mai kyau da daddare saboda Fargaba da tsoro da yake addabansu,
Idan bakuyi haka ba wallahi ku tabbata kunci Amanan Talakan Nigeria da Masoyan ku.
Allah kawo mana karshen wannan Masifa ya Kawo mana zaman Lafiya da Kwanciyar hankali.”







