TSOHON BANZA DA FYADE : Karanta Yadda wannnan Tsohon Banza Mai shekara 80 Yayiwa Mai shekara 10 Fyade
Daga : Datti Assalafiy
Rundinar ‘yan sandan Nigeria reshen jihar Yobe ta kama wani tsohon biri tsohon banza mai suna Muhammad Bara’u ‘dan shekara 80 wanda yake da zama a gundumar Lawan Fanni garin Gashua jihar Yobe
‘Yan sanda sun kama wannan tsohon banza ne bisa laifin aikata fyade da ya yiwa wata yarinyar marainiya ‘yar shekara 10, inda ya yaudareta da mintin cakulet ya aikata cikin dakinsa domin ta dauko masa wani abu, sai yabi bayanta ya danneta ya mata fyade
Gwajin da Likitoci suka yiwa marainiyar ya nuna tsohon banzan ya shigeta, sannan tsohon birin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, zuwa gobe za’a kai tsohon sashin binciken manyan laifuka (State CIID) na jihar Yobe dake garin Damataru, idan an kammala bincike sai a gurfanar dashi a gaban kotu
Hakika rayuwar wannan mutumin banza batayi albarka ba, dama ance ba farkon ba karshen
Jama’a ku gargadi yaranku da kannenku mata, kada su kuskura wani namiji ya aikesu dakinsa su yadda, lura da cewa yawanci masu aikata fyade suna yaudaran yara mata ta hanyar aikansu zuwa inda suke so gurin da ba kowa su danne su
Yaa Allah Ka karemu daga yin mummunan karshe Amin

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)







