Kotu ta yanke wa Sadiya Haruna hukuncin komawa Islamiyya
Yau Litinin rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da wata mai amfani da kafafen sada zumunta Sadiya Haruna a gaban kotu.
An gurfanar da ita a kotun shari’ar Musulunci da ke hukumar Hisbah, bisa zargin yaɗa batsa a kafafen sada zumunta.
Yayin zaman kotun mai shari’a Ali Jibrin Ɗanzaki ya yanke mata hukuncin sanyata a makarantar Islamiyya ta Darul Hadith har tsawon wata shida.
Kamar yadda freedom radio na ruwaito. Za ta riƙa zuwa kullum tare da rakiya jami’in hukuma.


Hoto : Instagram
Daga: sadiya haruna
Sannan za ta riƙa sanya hannu a duk sanda ta je.
Sadiya Haruna dai ta shahara a kafafen sada zumunta wajen yaɗa hotuna tare da kalaman batsa.


Tun da farko rundunar ƴan sandan jihar Kano ce, ta karɓi ƙorafi daga mutane kan ayyukan matashiyar.


