Labarai

Rahoto : An kashe Boko haram/ISWAP 126 a harin Operation Desert sanity A Jihar Borno

Zuwa yanzu rahotanni sun bayyana cewa an kashe yan boko Haram/ISWAP 126 a harin da Operation Desert Sanity na daya da na biyu suka yi a arewa da yammacin Jihar Barno Aliyu Samba ne ya ruwaito a shafin na Facebook
Sojoji goma sun rasa ransu sakamakon harin kamar yadda Col. Obinna Azuikpe, Wanda shine ko’odinetan rukunin Theartre Command Intelligence.
Ƴan ta’addan sun yi hari takwas da motar bam a Maiduguri, Malam Fatori, Gamborun Ngala da kuma karamar hukumar Bama tsakanin watan Janairu zuwa Maris din shekara ta 2022.
Yan boko Haram/ISWAP da baza su gaza 50,801 tare da iyalansu sun miƙa wuya ga dakarun Operation Haɗin Kai a arewa maso gabashin Najeriya tun daga watan Satumba 2021 zuwa yau, kamar yadda Manjo Janar Christopher Musa, Theatre Commander, Operation Hadin Kai (OPHK) ya fada a ranar juma’a.
Wadanda suka mika wuya ɗin sun haɗa da mayaka 11,349, mata 15,289 da kuma yara ƙanana guda 24,163.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button