Tsohon Sarki Sanusi Zai Fara Koyarwa A Jami’ar Oxford
Daga Oktoba na wannan shekara, tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II zai fara wata taƙaitacciyar koyarwa a Jami’ar Oxford dake Birtaniya.
Kwamitin Gudanarwa na Cibiyar Nazarin Afirka ta Jami’ar Oxford ya amince da buƙatar Mista Sanusi ta zama Malami Mai Ziyara a Cibiyar daga shekarar karatu ta 2020-2021, kamar yadda jaridar Intanet, Kano Focus ta rawaito.
Shafin najeriyarmu a yau na sun ruwaito cewa,Cibiyar Nazarin Afirka ta Jami’ar Oxford tana ɗaya daga cikin manya-manyan Cibiyoyin Nazarin Afirka na duniya.
Cibiyar ta lura da cewa Mista Sanusi, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya ne, CBN, yana so ya yi amfani da wannan lokaci don rubuta littafi a kan: “Yadda Babban Bankin Najeriya Ya Tunkari Durƙushewar Tattalin Arziƙin Duniya: Nazari A Babban Bankin Najeriya 2009-2013”.
Zai yi wannan aiki ne bisa gogewarsa a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, kuma a matsayin ma’aikacin banki.
Cibiyar ta horar da ɗalibai masu digirin farko waɗanda a yanzu suna riƙe da muhimman muƙamai a ɓangarorin da suka shafi zamantakewa , tattalin arziƙi da siyasa a Afirka da sauran sassan duniya.
Cibiyar da take da ƙarfi a Kimiyyar Zamantakewa da Al’amuran Bil’adama, tana shan yabo sakamakon ingancin aiki, bincike-bincike masu taka rawa a fagen ilimi da shirya manufofin al’umma.
Mista Sanusi, Masanin Tattalin Arziƙi kuma ma’aikacin banki, ya zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN daga 2009-2014.
Mujallar Banker ta saka shi a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Mafi Hazaƙa a 2010 sakamakon sauye-sauye da ya kawo da kuma yaƙi da cin hanci a ɓangaren banki, abu na farko a lokacin da tattalin arziƙin duniya ya shiga ruɗani.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




