Mutum Biyu Sun Sayi Fom Din Takarar Gwamna Karkashin Jam’iyyar PDP A Jihar Borno, Domin Su Fafata Da Gwamna Zulum A Zabe Mai Zuwa
Daga Comr Abba Sani Pantami
Wasu jiga-jigai a jam’iyyar hamayya ta PDP sun yanki fam din shiga takarar gwamna a jihar Borno, da nufin yin takara a zabe mai zuwa.
Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu 2022, wadannan ‘yan siyasa za su nemi su kifar da gwamnatin APC mai-ci.
Muhammed Imam da Muhammed Ali sun biya N21m, sun mallaki fam din takarar kujerar gwamnan jihar Borno a jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Rahoton ya ce wadannan ‘yan siyasa sun kammala cike fam din, kuma sun dawo da shi ga jam’iyya, su na sauraron ranar zaben fitar da gwani.
Hakan na zuwa ne bayan an yi ta yada labarai cewa an rasa wani ‘dan siyasa da zai kalubalanci Farfesa Babagana Umara Zulum wanda yake kan mulki.
A 2019, Imam ya yi wa PDP takara a Borno, ya samu kuri’a 66, 000 yayin da APC ta samu miliyan 1.17.
Wa kuke yiwa fatan Nasara a tsakanin su?