Labarai

Yadda Aka Yima Wata Budurwa Uwaila Fyade Sannan Aka Kasheta A Coci

Wata budurwa mai suna Vera Uwaila Omozuwa, mai shekaru 23, dalibar shekarar farko a bangaren ilmin kananun halittu(Microbiology) a jami’a UNIBEN dake cikin Benin City a jihar Edo ta gamu da ajalinta biyo bayan fyade da aka yi mata.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa dalibar ta kanje cikin cocin RCCG (Redeemed Christian Church of God) don yin karatunta a koda yaushe. A ranar laraba 27 ga Mayu, 2020, dalibar tana cikin karatu a cocin kamar yadda ta saba sai kwatsam taga wasu mutane marasa imani da ba’a san ko su waye ba sun shigo, inda suka yi mata fyade sannun suka kwala mata tukunyar kashe wuta (Fire extinguisher) inda a take kanta ya fashe wanda hakan yayi sanadiyyar zubar jini da yawa daga jikinta, kamar yadda ta bayyana kafin mutuwarta.
Mai gadin cocin tare da wasu mutane makwabtan cocin ne suka kaita babban asibitin koyarwa na jama’ar Benin, UNIBENTH inda a ranar asabar 30 ga Mayu 2020 da misalin karfe 10 na dare tace ga garinku nan.
Tuni dai jami’an yan sanda suka dukufa bincike don gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button