Labarai

Ɗan Shugaban kasa Buhari Zai Auri Ƴar Sarkin Bichi

Advertisment

Ɗan gidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, zai auri ‘ƴar Sarkin Bichi, Zahra Nasir Ado Bayero.
Wata majiya mai tushe ta bayyana wa majiyarmu ta Daily Nigerian cewar, za’a ɗaura Auren ne nan da Watanni 2 zuwa 3 masu zuwa.

Zahra Bayero

Zahra Bayero, wacce a yanzu haka take karatun Digiri a ƙasar Burtaniya, jika ce ga Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Dr. Ado Bayero.
Majiyar ta bayyana cewar, an jinkirta ɗaura Auren ne, saboda Mahaifiyar Angon, wato Aisha Buhari, ta je Birnin Dubai neman lafiya, inda ta shafe watanni 6 a can, kafin daga bisani ta dawo gida Najeriya.
-Majiya Idon Mikiya

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

3 Comments

  1. Alhamdulillah dama fatana shine baba buhari ya aurar da dukkan yayansa yana kan mulki Allah ya bada zaman lafiya in hakan ta faru na auren Yusuf Muhammad buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button