Labarai

Labari Mai Dadi : Bayan Sabani Da ‘Yan Majalisa, Buhari Ya Goyi Bayan Ministansa Akan Batun Daukar Ma’aikata 774,000

Daga Ibrahim Dau Mutuwa Dole

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin daukar ma’aikta na musamman da majalisar dokoki ta dakatar.

Gwamnatin ta sanar da kaddamar da shirin ta shafinta na Twitter a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da shirin wanda ma’aikatar kwadago ke jagorantar, daga cikin matakan rage radadin annobar korona.

Za a dauki mutum 1,000 daga kowani karamar hukuma 774 da ke kasar, sannan kwamitocin jiha za su kula da shirin.

“ An kaddamar da kwamitocin zaben ma’aikatan na jiha kuka sun fara aiki,” cewar gwamnatin tarayya ta shafinta na Twitter.

Keyamo ya yi cacar baki da majalisar dattawa a kan cewar su za su tsara
yadda daukar aikin za ta kasance.

Kwamitin majalisar tarayya a kan kwadago ya dakatar da fara diban aikin sakamakon hatsaniyar da ta shiga tsakaninsu da karamin ministan.

A wani taro da suka yi a watan Yuni, mambobin kwamitin sun kusa bai wa hammata iska tsakaninsu da ministan inda daga bisani suka koreshi daga majalisar.

Amma Keyamo ya zargesu da yunkurin kwace daukar aikin tare da son amshe guraben don amfanin kansu da makusantansu.

Ya kara da zargar ‘yan majalisar da kokarin kalubalantar hukuncin shugaban kasar.

Ya ce ‘yan majalisar sun dauki mataki da ya fi karfinsu.

The Cable ta gano cewa Keyamo ya samu ganawa da shugaban kasa inda ya bayyana mishi abinda ya faru a majalisar a kan shirin.

Shugaban kasar ya matukar fusata da yadda ‘yan majalisar ke son yin katsalandan a al’amarin da ya shafi
masu zartarwa.

Ya bukaci ministan da ya ci gaba da shirin kuma ya tabbatar da an yi shi bisa tsarin da ya dace na shari’a.

Ya kara da bukatar darakta janar na NDE da ya tsayar da duk wani tsari na daban a kan shirin wanda yake yi tare da kwamitin majalisar tarayya.

An kuma tattaro cewa, ministan shari’a, Abubakar Malami, ya rubuta wasika ga ‘yan majalisar da su kiyaye iyakokinsu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA