Labarai
Kalli Zafaffan Hotunan Motocin : Attajirin Najeriya Femi Otedola ya burge ‘ya’yansa da motocin Ferrari Portofino
Advertisment
Florence Ifeoluwa Otedola wadda aka fi sani da DJ Cuppy ta wallafa hotunan motocin da mahaifinsu ya saya musu a shafukanta na sada zumunta ranar Laraba.
Ta ce ya sayi motocin uku ne ga ‘ya’yansa uku – Tolani, Temi da Ifeoluwa Otedola.
Kiyasi ya nuna cewa ana sayar da Ferrari Portofino a kan $218,750 (N84,323,750.00).
Bbchausa sun kara da cewa bayanai daga Wikipedia sun nuna cewa Femi Otedola ya mallaki fiye da dalar Amurka 1.85 bn.
“Mahaifinmu ya kai mu cefanen motoci inda ya saya wa kowaccenmu mota daya!”, a cewar Temi Otedola a sakon da ta wallafa a Twitter.
Kalli yadda ‘ya’yan Otedola suka tsaya kusa da motocin Ferrari din da ya saya musu
Ana sayar da Ferrari Portofino a kan sama da naira miliyan tamanin da hudu
‘Ya’yan Otedola: Tolani, Temi da kuma Ifeoluwa kowaccensu ta samu mota daya kirar Ferrari Portofino
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com




![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)











