Duk Wanda Aka Kama Da Laifin Fyade za’a Dandaƙeshi kuma A Kasheshi (Hotuna) ~ Nasir El-rufai
Maigirma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sanya hannu a sabuwar doka na yin dandaka da kisa ga duk wanda aka kama da laifin fyade
Dokar na cewa:
Duk wanda yayi wa yarinya ‘yar kasa da shekara 14 fyade to za’a dandake shi, sannan a kashe shi
Duk wanda ya yiwa matar da ta haura shekaru 14 fyade za’a dandakeshi, sannan zai tabbata a gidan yari har karshen rayuwarsa, wato daurin rai da rai
Duk macen da ta yiwa namiji yaro fyade to za’a yi mata tiyata a cire kwayar halittar dake samar da koyin haihuwa a jikinta, wato itama za’a dandaketa
Duk yaron da bai balaga ba, ya yiwa yarinya fyade, za’a kama yaron a masa rijista cikin masu laifin cin zarafin mata, sannan za’a daukeshi a hoto a yadashi a kafofin watsa labarai da na sada zumunta ta yanda har abada duniya zata kalleshi a matsayin wanda ya taba aikata laifin fyade
Jinjina ga Maigirma gwamnan jihar Kaduna, Insha Allahu da wannan dokar muna sa tsammanin karshen masu aikata laifin fyade yazo a jihar Kaduna, muna fatan sauran gwamnoni zasuyi koyi da shi
Allah Ka kawo mana karshen wannan masifa na fyade Amin