Kwankwasiyya : Sama da mata dubu daya sunka yi zanga-zanga kan hukuncin kotu a kano
Kimanin mata sama da dubu daya ne suka gudanar da zanga-zanga a titunan Kano domin nuna damuwarsu kan cece-kucen da kotun daukaka kara ta yi, shafin gidan rediyo nasara radio fm na ruwaito.
Matan dauke da alluna suna rera wakokin goyon bayan gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf sun tunkari rundunar ‘yan sandan jihar inda suka mika takarda dauke da korafe-korafensu kan sakamakon hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.
Wannan shi ne karo na farko a tarihin Kano da mata suka zo da jama’a don yin maci kan tituna suna neman a yi wa dimokradiyya adalci tare da kare wa’adin zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris.
Daya daga cikin masu zanga-zangar lumana Hajiya Rabi Hotoro ta ce suna kan tituna domin nuna damuwarsu kan abin da ya faru a kotun daukaka kara.
Kano ta fada cikin tashin hankali na siyasa biyo bayan cece-kucen da aka samu daga shari’ar daukaka kara inda hukunci na magana da rubuce-rubuce ya banbanta.
Wani labari: Hon abdulmumin jibrin kofa ya karbi bakoncin malamai 1,000.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji dake Kano, Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, ya karbi bakuncin malamai 1,000 a kasar sa dake Kofa, Bebeji, ya Jagorancin dandazon Malamai domin gudanar da addu’o’i na musamman ga gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif na neman samun Nasara a kotun koli.
A zaman an karanta Alkur’ani Mai girma sau 1,101 tare da gabatar da addu’o’i na musamman.
Har ila yau, bayan kammala taron addu’ar, ya karbi bakuncin yara ‘yan firamare 5,000 a mazabarsa, kamar yadda ya saba yi, ya samar musu da kayan makaranta tare da tabbatar musu da kyawawan tsare-tsare na gwamnatin tarayya da na jihohi, musamman a kan shirin bayar da ilimi kyauta da ciyar da yara a makaranta.