Shehu Sani Ya Kalubalanci Tinubu, Sanatoci, Gwamnoni kan halin da ake ciki na tsadar Rayuwa a kasar


Tsohon dan majalisar Dattawa Daga jihar Kaduna Shehu Sani, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu, sanatoci, da gwamnonin jihohi da su sadaukar da kansu ga kasar nan.
Shehu Sani ya jaddada cewa bisa la’akari da halin kuncin da ake ciki a yanzu yana da matukar muhimmanci ga shugabanni su yi sadaukarwa domin ciyar da Najeriya gaba.
Da yake jawabi a wajen taron ministocin Baptist karo na 64 da aka yi a Kaduna, tsohon dan majalisar ya bayyana irin illar da hauhawar farashin man fetur ke yi a rayuwar yau da kullum ta ‘yan Najeriya.
Ya ce duk da cewa ci gaba yana bukatar sadaukarwa, amma bai kamata talaka ya dauki nauyinsa ba. Shehu Sani ya bukaci masu riƙe da madafun iko su zama abin koyi ta hanyar sadaukarwa.
“Mu kasa ce mai mutane miliyan 224, kuma ba za mu yi watsi da munanan kalubalen tattalin arziki da talakawa ke fuskanta ba,” in ji Shehu Sani. “Shugaban kasa, ministoci, gwamnoni, Sanatoci, da masu rike da madafun iko dole ne su jagoranci ta hanyar sadaukarwa domin ciyar da al’umma gaba.
– Ahmed Tijjani Ramalan