Faransa za ta fara raba wa ‘yan shekara 18 zuwa 25 kwaroron roba kyauta
Kowa da bukin zuciyarsa abunda ake kukan yayi karanci a wata kasa ga wata kasa ita fara rabawa yan kasar kyauta zatayi saboda yawansa kamar yadda rahoton BBCHausa na ruwaito.
Faransa na shirin rabawa matasa kwaroron roba kyauta farawa daga watan Janairu, a wani yunkuri na rage ƴaduwar cutuka da ake samu daga jima’i.
Shugaban ƙasar ta Faransa, Emmanuel Macron ya sanar da matakin ne a ranar Alhamis, a wani bikin kan lafiya da aka shiryawa matasa.
Macron ya ce matasan za su iya samun kwaroron robar ne a shagunan sayar da magani, inda ya kwatanta hakan da kaucewa kamuwa da cutuka.
A 2020 zuwa 2021, Faransa ta samu ƙaruwar masu kamuwa da cutukan da ake dauka daga jima’i da kashi 30.
A cikin 2018 gwamnatin Faransa ta fara biyan kuɗin kwaroron roba ga daidaikun mutane, idan an saya a kantin magani tare da takardar magani daga likita ko ungozoma.