Yadda Maihaifiyar Maryam Sanda Ta Auri Mahaifinta
Daga Anas Abubakar Dan Aunai
Hajiya Maimuna Aliyu mahaifiya ga Maryam Sanda matar marigayi Bilyaminu Bello Halliru ‘yar asalin garin Izge ce dake karamar hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Ta hadu da Alhaji Sanda mahaifin Maryam a wani gurin sayar da abinci inda a nan ne take sana’ar sayar da abinci, ya aureta ne tana da takardar shaidar karatun sakandare inda ya karfafa mata gwuiwar karo karatu a Jami’ar Maiduguri, inda ta karanci fannin lissafin kudi (Accounting).
Bayan ta shiga Jami’ar sai al’amura suka sauya inda mazaje suka rika nuna sha’awarsu akan ta suna bin ta saboda kyawun surarta da nuna rayuwar kasaita da take yi.
Bayan ta kammala karatunta sai ta fara aiki da wani banki, inda aikin ya kai ta Abuja kuma ya kusanta ta tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a harkar tsaro lokacin mulkin Jonathan watau Andrew Azazi wanda ya rasu sakamakon hadarin jirgin sama, inda take kula harkokin kudinsa.
Bayan mutuwar Azazi sai ta sake gina sabuwar rayuwa, inda aikin banki ya kai ta Nguru bayan dan lokaci ta sake komawa Abuja da yara uku da suka haifa da Alhaji Sanda, ciki har da Maryam. Amma kuma mijinta Alhaji Sanda bai yarda ya bi ta ba, daga nan kuma rigimar ‘ya’ya ta shiga tsakaninsu, har abin ya kai su ga sai da kotu ta shiga tsakaninsu da Hajiya Maimuna ta yi amfani da Masu Gidan Rana (Kudi) aka bar mata yaran, kuma kotu ta sa ya sake ta aka raba auren.
Basu dade a Abuja ba Hajiya Maimuna ta sa aka yi wa yaran canjin makaranta daga Jami’ar Maiduguri zuwa wata Jami’ar a birnin London, inda a nan ne Maryam ta hadu da Bilyaminu dan tsohon shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Bello Halliru.
©Zuma Times Hausa